Kofin Duniya:Faransa Da Mali Za Su Kara A Wasan Gab Da Na Karshe

Wasan Argentin da Brazil

A ranar Talata Jamus za ta fafata da Argentina a gasar wacce ake yi a kasar Indonesia.

‘Yan wasan Faransa da Mali za su fafata a zagayen wasannin semifinals a gasar cin kofin duniya ta ‘yan kasa da shekaru 17 bayan da dukkansu suka samu nasara a wasannin da suka buga a ranar Asabar.

A ranar Talata Jamus za ta fafata da Argentina a gasar wacce ake yi a kasar Indonesia.

Faransa ta doke Uzbekistan bayan da Isma’il Bouneb ya zura kwallon da ta ba ta nasara minti bakwai kafin a kammala wasa.

Ita dai Mali Morocco ta doke yayin da Argentina ta lallasa masu rike da kofin gasar wato Brazil da ci 3-0 inda kyaftin din Argentina Claudio ya zura dukka kwallaye uku.

A ranar Juma’a Argentina ta doke Brazil mai rike da kofin gasar d ci 3-0 inda kyaftin Claudio Echverri ya zura duka kwallayen.