Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Haaland Ya Gurde Kafa A Karawar City Da Bournemouth


Haaland
Haaland

Manajan City Pep Guardiola ya ce ya yi wuri a tantance ko Haaland zai samu damar buga wasan City da Young Boys a gasar cin kofin Zakarun Turai a ranar Talata.

Dan wasan Manchester City Erling Haaland ya gurde kafarsa a karawar da City ta yi da Bournemouth.

City ta lallasa Bournmouth da ci 6-1 a ranar Asabar.

An cire Haaland a daidai hutun rabin lokaci bayan da ya gurde kafar tasa.

Manajan City Pep Guardiola ya ce ya yi wuri a tantance ko Haaland zai samu damar buga wasan City da Young Boys a gasar cin kofin Zakarun Turai a ranar Talata.

Ya kara da cewa ya cire shi ne a matsayin kandagarki gudun kada raunin nasa ya tsananta.

City dai ba ta bayyana kafar da Haaland dan asalin kasar Norway ya samu raunin ba

Dan wasan gaban ya zura kwallaye 13 a wannan kakar wasa a dukkanin gasar da ake bugawa.

A makon jiya ya zura kwallo biyu a dokewar da City ta yi wa Manchester United da ci 3-0.

Dandalin Mu Tattauna

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG