Fafaroma Francis Ya Kai Sakon Zaman Lafiya A Afirka Ta Tsakiya

Fafaroma Francis Ya Kai Sakon Zaman Lafiya A Afirka Ta Tsakiya

Fafaroma Francis ya je Afirka ta tsakiya yau Talata domin kai sakon zaman lafiya ga kasashe biyu da ke fama da tashe-tashen hankula a yankin.

WASHINGTON, D.C. - Fafaroman mai shekaru 86 da haifuwa ya kai ziyarar kwanaki shida a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, inda zai jagoranci wani taro a filin jirgin sama na N’dolo da ke Kinshasa babban birnin kasar, wanda ake sa ran zai samu halartar mutane sama da miliyan daya.

Fafaroma Francis Ya Kai Sakon Zaman Lafiya A Afirka Ta Tsakiya

Fafaroma Francis Ya Kai Sakon Zaman Lafiya A Afirka Ta Tsakiya

Francis kuma ya samu tarba daga dubun-dubatar 'yan kasar Kongo wadanda suka yi layi a babbar hanyar shiga cikin birnin, mutane a jere da kuma yara sanye da kayan makaranta suna sahun gaba.

Akalla rabin mutane Kongo miliyan 95 membobin Cocin Roman Katolika ne, wanda hakan ya sa ta zama al'umma mafi girma a Cocin a Afirka.

Fafaroma Francis Ya Kai Sakon Zaman Lafiya A Afirka Ta Tsakiya

Sai dai Majalisar Dinkin Duniya ta ce kimanin mutane miliyan 5 da dubu 700 ne suka rasa matsugunansu a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, sakamakon yakin da aka shafe shekaru ana gwabzawa a yankin Arewacin Kivu, tsakanin dakarun gwamnati da kungiyar 'yan tawayen M23, da kuma hare-haren kungiyoyin da ke da alaka da kungiyar ISIS ta ta’adda.

-AP