Fadawar Afghanistan Hannun Taliban Babban Abin Takaici Ne - Amurka

Mayakan Taliban a radar Lahadi a burnin Kabul 15 ga watan Agusta, 2021. (AP Photo/Sidiqullah Khan)

Blinken ya kore duk sukar da ake yi wa hukumomin Washington cewa ba su kimtsa da kyau ba, duba da yadda rundunar dakarun Afghanistan ta durkushe cikin sauri.

Babban jami’an diflomasiyyar Amurka ya kwatanta fadawar kasar Afghanistan hannun Taliban da karbe ikon birnin Kabul a matsayin “babban abin takaici,” yana mai cewa Amurkan ta tashi haikan wajen ganin dukkan Amurkawa da ‘yan Afghanistan da suka taya su aiki sun fice daga kasar.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken a ranar Lahadi ya ce lafiyar Amurkawa wadanda wasun su na ofishin jakadancin Amurka da ‘yan Afghanistan da suka taimaka masu, shi ne abu muhimmi a gare su.

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken

Blinken ya kuma kore duk sukar da ake yi wa hukumomin Washington cewa ba su kimtsa da kyau ba, duba da yadda rundunar dakarun Afghanistan ta durkushe cikin sauri.

Amurka za ta yi “duk abin da ya kamata mu ga cewa mun fitar da su idan hakan suke so.” Blinken ya fadawa CNN a shirin “State of the Union.”

“Ba mu tambayi kungiyar Taliban wani abu ba,” Blinken ya kara da cewa, yana mai jaddada cewa, “amma mun fada masu cewa idan har suka kawo cikas ga jami’anmu da ayyukanmu a daidai wannan lokaci, za mu mayar da martani ba da bata lokaci ba.”

A gefe guda, wani jami’in Amurka wanda ya nemi a sakaya sunansa saboda yanayin da ake ciki, ya fadawa VOA cewa, “ana kan” kwashe duk jami’an diflomasiyyar da ke ofishin jakadancin Amurka a Kabul.

Jirgin Amurka mai saukar ungulu yana shawagi a saman ofisin jakadancin Amurka da ke Kabul

Jami’in ya kara da cewa, dubban dakarun Amurka na kan isa kasar ta Afghanistan kuma suna “rike” da yankunan ofishin jakadancin da kuma filin tashin jirage na Hamid Karzai da ke wajen birnin Kabul.

Wani babban jami’in gwamnatin Amurka ya kuma fadawa VOA cewa, ana sanar da shugaba Joe Biden abin da ke faruwa akai-akai, yayin da yake zaune a Camp David.

A ranar Asabar Biden ya ba da umarnin ya tura karin dakaru 1,000 zuwa Kabul don su taimaka wajen kare muradun Amurka su kuma fitar da jami’anta da wasu ‘yan Afghanistan da suka yi wa Amurka aiki.

Cikin ‘yan kwanaki masu zuwa, ana sa ran dakarun Amurka 4,000 za su isa birnin Kabul don agazawa sojojin Amurka da yanzu adadinsu bai wuce 650 bayan da aka janye da yawa daga cikinsu.