An fara rikicin ne tun daga yammacin ranar Lahadi a garin Jalalabad da ke gabashin Afghanistan.
Aƙalla mutum 29, ciki har da fursunoni, sun mutu, yayin da kusan 50 suka jikkata, a cewar Ataullah Khogyani, kakaki agwamnatin Lardin Nangarhar.
Wata kungiya mai ikrarin jihadi mai suna ISIL ce ta dauki alhakin harin ta kafar kamfannin dillancin labaranta, harin da ya fara da tayar da bam sannan ya biyo baya da ‘yan bindiga da suka kutsa kai cikin gidan yarin.
Khogyani ya ce jami'an tsaro sun yi nasarar sake kama fursunoni akalla 1000 yayin da suke kokarin tserewa amma bai ce ko akwai wadanda suka tsere a cikin fursunonin ba.
Ya kuma tabbatar da cewa aƙalla maharan uku sun mutu amma wasu da yawa suna makale a cikin gidan yarin ko kuma a gine-ginen da ke kusa, inda suke ci gaba da kai wa jami'an tsaro hari.
A cewar jami'an lardin, sama da fursunoni 2,000 ne a cikin gidan yarin a lokacin da aka kai wannan hari.
Wani ganau mai suna Sohrab Qaderi ya sheda wa kamfanin dillancin labarai cewa an saka dokar zama a gida a Jalalabad yayin faruwar lamarin.
Facebook Forum