Jiya Asabar jami’ai a kasar Afghanistan sun ce wani bam da aka dana a gafen hanya a arewa maso gabashin kasar a lardin kan iyaka na Badakhshan ya yi sanadin mutuwar ‘yan sanda akalla goma sha daya.
Harin bam din na zuwa ne a daidai lokacin da manzon Amurka na zaman lafiya, Zalmay Khalilzad ,ke kai wata ziyara a yankin a kokarinsa na ganin an cimma jituwa a siyasance tsakanin bangarorin da ke fada a Afghanistan.
(Wasu mayakan Taliban)
Wani mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan lardin ya gaya ma Muryar Amurka cewa harin, wanda aka kai da dare, an auna shi ne kan wata tawagar jami’an tsaro da ke gaggauta zuwa gundumar Khash don taimaka ma wasu sojoji da ke yaki da ‘yan tawayen Taliban a can.
Sanaullah Ruhani ya ce daga cikin jami’an tsaron da su ka mutu har da wani babban jami’in ‘yan sandan wurin. Ya kara da cewa jami’an tsaron gwamnati sun hallaka ‘yan Taliban da dama a yayin wannan tashin hankalin na daren Jumma’a a Khash, inda har su ka kashe wani shugaban ‘yan tawayen.
Facebook Forum