Da kakkausan lafazi Shugabannin Afghanistan da na Amurka sun yi Allah wadai da harin bom din da ya faru a Kabul babban birnin Afghanistan ranar Asabar 7 ga watan Nuwamba, wanda ya yi sanadiyyar kisan manyan jami’an babban bankin kasar, daya daga cikinsu wani sanannen tsohon mai gabatar da shirye-shirye ne a wata tashar talabijin.
‘Yan sanda sun ce wani abun fashewa mai maganadisu ne ya tashi a wata mota da ke dauke da mataimakin shugaban gudanarwa na bankin DAB na Afghanistan, da abokin aikinsa Yama Siawash, wanda ya yi aiki a tashar talabijin din TOLO TV mai zaman kanta. Haka shi ma direban da ya tuka motar ya mutu.
Nan take dai babu wanda ya dauki alhakin kai harin, amma ministan cikin gida na Afghanistan ya dora laifin kan wasu 'yan bindiga, da ake kira yan Haqqani, da ke da alaka da kungiyar Taliban.
Harin na jiya Asabar shine na baya-baya a tarin kashe-kashen manyan jami’ai da kuma wasu mutane da aka auna da Kabul ta fuskanta a 'yan makonnin nan.
Facebook Forum