Facebook Ya Amince Yana Musayar Bayanan Kwastamominsa

Facebook

Kamfanin Facebook ya tabbatar da kulla yarjejeniyar musayar bayanai da wasu kamfanonin fasaha na kasar China guda hudu.

An gano a cikin kamfanonin akwai wanda ke yin barazana ga tsaron Amurka a cewar sashen tattara bayanan sirrin kasar, lamarin da ya sake haifar da damuwa ga yanda babban kamfanin sada zumunta ke rike bayanan mutane.

Amincewar da kamfanin sada zumunta na nan Amurkar ya yi a jiya Talata, na zuwa ne wuni biyu bayan da jaridar New York Times ta bankado yarjejeniyar musayar muhimman bayanai da Facebook ya kulla da kamfanonin masu kera na'urorin fasaha da suka hada da Huawei da Lenovo da OPPO da kuma TCL, saboda masu amfani da Facebook su samu saukin bude shafinsu a kan na'urori da dama.

Jami'an leken asirin Amurka sun dauki shekaru da dama suna nuna damuwarsu a kan Huawei, da cewa gwamantin China zata iya kokarin satar bayanan mutane dake hannunta. Wannan damuwa tasa ma'aikatar sojan Amurka ta haramta sayar da wayoyin zamani na Huawei a tashoshinta

Mukaddashin shugaban Facebook mai kula da huldan wayar hannu, Francisco Varela ya fada a jiya Talata cewa yarjejeniyar musayar bayanai da Huawei da kuma sauran kampanonin China ana kula da ita tun daga farko.