Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Zata Kakabawa Kasashen Dake Hulda Da Iran Takunkumi


Steve Mnuchin, sakataren kudin Amurka
Steve Mnuchin, sakataren kudin Amurka

Sakataren kudin Amurka Steve Mnuchin ya ce kasashen da suka ci gaba da yin hulda da Iran zasu fuskanci takunkumi koda ma kawayen Amurkan ne

Kasashe kawayen Amurka za su fuskanci hadarin gaske, muddun su ka cigaba da yin hulda da Iran, ciki har da yiwuwar fuskantar takunkumi daga Amurka.

Ma’aikatar kudin Amurka ta yi gargadi jiya Talata cewa har yanzu Iran na amfani da wasu kamfanoni don bad da sawu, ko ma bayan da ta rattaba hannu kan yarjajjeniyar nukiliya ta 2015, jami'an gwamnatin Amurka sun ce su na kyautata zaton Iran za ta cigaba da yin hakan.

A watan jiya Shugaba Donald Trump ya ba da sanarwar cewa Amurka za ta janye daga yarjejjeniyar nukiliya ta 2015 wadda aka cimma tsakanin manyan kasashen duniya da Iran, ya na mai kiranta "yarjajjeniya mai amfanar bangare guda, wadda bai ma kamata a ce an yi irinta ba."

Ya kuma umurci dukkan hukumomin Amurka da su sake kakaba takunkumi kan Iran.

To amma kasashen Turai na jan kafa wajen yin watsi da yarjejjeniyar, muddun dai Iran ta cigaba da mutunta ka’idodinta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG