Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Salon Gwamnatin Trump Na Jefa Amurkawa Cikin Talauci -MDD


Donald Trump, shugaban Amurka
Donald Trump, shugaban Amurka

Bincike da Philip Alston na ofishin hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya ya gudanar ya gano cewa manufofin gwamnatin shugaban Amurka, Donald Trump na kara jefa Amurkawa cikin kuncin talauci

Wani mai bincike kan hakkin dan Adam a Majalisar Dinkin Duniya, ya gano cewa, tsare-tsaren da gwamnatin shugaba Trump ke amfani da su wajen gudanar da harkokin mulki, na kara tilastawa Amurkawa shiga kangin talauci.

Ofishin hakkin dan adam na Majalisar Dinkin Duniya a jiya Litinin ya ce, Philip Alston, wanda jami’i ne na musamman mai dauko rahoto kan batutuwan da suka shafi tsananin talauci, ya kwashe watanni yana ziyartar sassan Amurka.

Ya kuma hada wani rahoto kan yadda gwamnatocin da suka gabata, suka bar jama’ar kasar cikin halin kunci.

Yayin da yake shirin gabatar da rahoton ga Majalisar Dinkin Duniya a wata mai zuwa, Alston, ya kalublanci gwamnatin shugaba Trump kan matakin da ta dauka na rage kudaden haraji, matakin da ya ce ya bai wa masu hanu da shuni da manyan kamfanoni garabasa, ya kuma kuntatawa talakawa.

Shi dai Alston, ya ziyarci yankunan marasa galihu a Alabama, California, Georgia, Puerto Rico, West Virginia da kuma nan Washington DC.

Sai dai a jiya Litinin, wani jami’in da ke wakiltar Amurka a Majalisar Dinkin Duniya a Geneva, ya ce, gwamnatin ta Trump, ta dukufa ne wajen samarwa da daukacin jama’ar kasar hanyoyin samun kudaden shiga.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG