Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Zargin Paul Manafort da Tuntubar Wasu Shaidu


Tsohon mai bincike na musamman Robert Mueller ya zargi Manafort da yin magana da wasu shaidu akan binciken da ake yi mashi.

Masu gabatar da kara dake yiwa mai bincike na musamman Robert Muller aiki sun ce tsohon manajan yakin neman zaben shugaba Donald Trump Paul Manafort, ya sha kokarin ya tuntubi shaidun dake da alaka da batun manyan laifuffukan da ake tuhumar sa da su.

A wani zaman kotu da aka yi jiya Litinin, masu gabatar da karar sun ce Manafort da daya daga cikin abokan aikinsa sun sha tuntubar shaidu a wani yunkuri na fada masu abinda za su ce a binciken. A watan Fabarairu ne suka tuntubi shaidun, jim kadan bayan da wani alkali ya sake dago batun laifin da ake tuhumar Manafort da shi a lokacin da yake tsare a gidansa.

Ba a ambaci sunayen shaidun ba a zaman kotun da akayi, amma masu gabatar da karar sun ce mutanen sun yi aiki da Manafort wajen hada wata kungiyar tsofaffin jami’an kasashen Turai, da ake kira Hapsburg Group da turanci, dake yada muradan Ukraine a kasashen Turai da kuma Amurka. Ana tuhumar Manafort da laifuffuka, ciki harda kamun kafa ba bisa ka’ida ba dangane da kungiyar ta Hapsburg.

Facebook Forum

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG