A yau dandali ya sami zantawa da wasu 'yan mata ne dangane da yadda 'yan mata matasa ke kwaliya a wannan yanayi na zafi, koda shike wasu daga cikin 'yan matan sun bayyana cewa an rage yawan yin kwaliya saboda rashin ruwa da kuma yanayi na zafi da ake fuskanta a yanzu.
Amfani da turare da sauran kayan kamshi nada fa'ida a kowanne lokaci kamar yadda yawancin 'yan matan suka fada domin kuwa yakan taimaka wajan rage warin zufa da sauran su.
Rashin isashshen ruwa da wutar lantarki yasa 'yan mata da yawa sun rage yawan kwalliya amma a cewar su, hakan bazai hana su amfani da turare ba domin koda mutum ya dade a cikin rana kamshin turaren zai taimaka wajan rage warin zufa.
Daga karshe sun yi kira ga sauran 'yan mata musamman yadda aka sami sauyin yanayi na zafi, cewar kada su yi kasa a gwiwa wajan tabbatar da tsabtace jiki domin masu iya magana sun ce tsabta cikon addini ce.
Ga cikakkiyar hirar.