El Rufai Ya Ce Hare-haren 'Yan Bindiga Sun Fi Na Boko Haram Muni

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-Rufa'i a taron kwamitin zartarwar jihar

Gwamnatin jihar Kaduna ta ce an kashe mutane 1,129) a fadin jihar Kaduna a bara, sannan an kiyasta cewa kullum akan sace mutane tara a fadin jihar.

Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmed El-rufa'i wanda ke jawabi a wajen taron gabatar da rahoton tsaro na shekarar 2021, ya ce rahoton ya tabbar da cewa akwai aiki gaban mahukunta.

El-rufa'i ya ce ya kamata gwamnati ta dauki tsauraran matakan tsaro kan hare-haren 'yan-bindiga a Arewa maso yamma fiye da yadda ta yi kan 'yan- Boko Haram.

Ganin yadda rahoton tsaro na gwamnatin jihar Kadunan ya dada tabbatar da ta'azzarar matsalar tsaro ya sa masani kan harkokin tsaro, Manjo Yahaya Shinko mai ritaya jawo hankali don samun mafita.

Rahoton tsaro na shekarar 2021 da gwamnatin jihar Kaduna ta gabatar dai ya nuna cewa kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Igabi, Chukun da Zangon Kataf su ne su ka fi adadin wadanda 'yan-bindigan su ka hallaka a bara.