Duk da kubutar da wasu matafiya a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna da jami'an tsaro su ka ce sun yi, wasu wadanda su ka tsira sun ce 'yan-bindigan sun kwashe mutane da dama sannan su ka kashe wasu.
Hanyar Kaduna-zuwa Birnin Gwari dai ta dade ta na fama da hare-haren 'yan-bindigan da kan tare hanyar da tsakar rana.
Sai dai tare hanyar da suka yi a ranar Laraba ya yi wa 'yan-bindigan tutsu saboda da yawan matafiyan sun kubuta.
Wasu mata da su ka tsira wadanda su ka nemi mu sakaya sunansu, sun bayyana abin da ya faru.
“Mun wuce motoci kamar fiye da talatin, mun yi nisa muna kawo unguwar yako sai ga su barayin sun fito, to a lokacin da direban mu zai yi kwana ashe mun riga mun wuce gate din farko, in waiga haka sai na ga wasu ana ace musu mu je, shi ne na rabe na dawo hanya wajen motoci sai ga sojojin sun iso.”
Ita ma wata mata da harin 'yan-bindigan ya ritsa da ita dauke da dan ta goye ta yi bayanin yadda ta tsira.
“Goggo na ta ce in bude mota, shima direban ya ruga da gudu, sai na wurga yaron can kasa nima sai na fada mishi, yana ta kuka sai na ga mutane da yawa sun wuce cikin daji nima sai na bi su
Kokarin jin ta bakin jami'an tsaro dai ya ci tura, sai dai mai magana da yawun rundunar sojan saman ya ce “sojan saman ne su ka ceto mutane 26 daga cikin wadanda 'yan-bindigan su ka yi yunkurin sacewa.
Ko da yake, masani akan harkokin tsaro, Dafta Yahuza Ahmed Getso ya ce rashin kayan aiki ga jami'an tsaro ne ke kawo koma baya.
Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara: