Eguavoen Bai Yi Murabus Daga Horas Da Super Eagles Ba – Peterside

Augustine Eguavoen (Facebook/Super Eagles)

Wani tsohon mai tsaron ragar kungiyar Super Eagles, Idah Peterside, ya bayyana cewar Augustine Eguavon ya tabbatar masa da cewa bai yi murabus daga zama mai horas da babbar kungiyar kwallon kafar Najeriya ba.

Sakamakon tashi babu nasara (ci 0-0) a karawar da Najeriya tayi da kasar Rwanda ta neman cin kofin nahiyar Afrika a jiya talata, an yi ta yada rade-radi cikin dare na cewar Eguavoen, wanda a baya-bayan hukumar kula da wasan kwallon kafar Najeriya (NFF) ta nada domin ya jagoranci kungiyar bayan kasa cimma matsaya da bajamusen mai horaswa Bruno Labaddia, shima ya ajiye aiki.

Amma da yake zantawa a shirin hantsi na tashar talabijin ta Channels mai taken “Sunrise Daily” na yau Laraba, Peterside yace Eguavoen ya musanta rade-radin a wata hira da ya yi dashi ta wayar tarho.

Tsohon golan na Super Eagles ya kara da cewa bayan samar da daidaito a kungiyar a wasanni 2 da ta buga a baya-bayan nan, Eguavoen zai cigaba da daidaita al’amuranta, kasancewar ‘yan wasan sun san shi sarai.