KADUNA, NIGERIA - Daga daren Asabar zuwa asubahin Lahadi ne dai hukumar kula da tsara birane ta jihar Kaduna wato KASUPDA ta fara aikin rushe-rushen wasu gine-ginen da ta ce an yi su ba bisa ka'ida ba kuma a ciki har da gine-ginen mabiya shi'a da ke jihar Kaduna.
Mabiya shi'ar dai sun kira taron manema labarai da su ka ce ba su lamunci rushe-rushen ba amma sai gashi a jiya Litinin ma gwamnatin ta sake rushe wata makarantar mabiya shi'ar da ke garin Maraban Jos.
Malam Abdullahi Umar Maraban Jos, wanda ke kula da makarantar ya ce gwamnatin ba ta sanar da su laifin su ko basu dalili.
Umar ya ce su na zaman-zaman su kawai sai ga hukumar kula da tsara birane ta jihar Kaduna tare da jami'an tsaro wadanda su ka kama harbe-harbe kafin su ka rusa makarantar ba tare da wani bayani ba.
Kafin rushe wannan makaranta ma mabiya shi'ar na jihar Kaduna sun ce gwamnatin ta rushe musu wasu gine-gine, kuma Malam Aliyu Umar Turmizi shi ya jagoranchi mabiya shi'ar zuwa gaban manema labarai.
Sai dai gwamnatin jihar Kaduna ta ce gine-ginen da aka yi ba bisa ka'ida ba ta ke rusawa ba kadai na mabiya shi'a ba, inji Mai magana da yawun hukumar kula da tsara birane ta jihar Kaduna, Malam Nuhu Garba Dan-Ayamaka.
Ya ce babban abun da hukumar ke la'akari da shi shine cika ka'idojin gini da kuma samun izini saboda haka duk gine-ginen da hukumar ta rusa sun sabawa ka'ida ne.
Da yake gine-ginen Mabiya shi'ar 48 ne gwamnatin ta sanar da shirin rushewa, Malam Abdullahi Umar Maraban ya ce za a dauki matakai.
Dama dai ruwa ya yi tsami tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da mabiya shi'a tun shekarar da su ka sami matsala da tawagar sojan Najeriya wanda daga baya gwamnatin ta sa aka rushe babban cibiyar mabiya shi'ar da ke Zaria.
Saurari cikakken rahoto daga Isah Lawal Ikara:
Your browser doesn’t support HTML5