Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Har Yanzu Ba A San Inda Masu Ibada 20 Da Aka Sace A Wata Coci A Kaduna Suke Ba 


Cocin da aka yi garkuwa da mutane
Cocin da aka yi garkuwa da mutane

Kungiyar Kiristocin Najeriya ta CAN ta ce tana ci gaba da neman mutane 20 da wasu ‘yan bindiga suka yi garkuwa da su a wata coci yayin da suke gudanar da ibadar ranar Lahadi a jihar Kaduna.

Kungiyar CAN ta ce wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki a wata coci da ke wajen birnin Kaduna inda suka tafi da mutane sama da 40 amma daga baya suka saki wasu.

Jihar Kaduna na daga cikin jihohin Najeriya da suka fi fama da ‘yan bindiga da ke yawan satar mutane domin neman kudin fansa.

A ranar Talata shugaban kungiyar CAN reshen jihar Kaduna ya ce kimanin mutane 42 ne ke cikin cocin a safiyar Lahadi kafin maharan su mamaye cocin inda suka tafi da dukkan masu ibadar, ciki har da mata da kananan yara.

Ya kuma ce daga baya ‘yan bindigar sun sako mutane 22 daga cikinsu, amma suna ci gaba da garkuwa da sauran mutun 20.

Rabaran Joseph Hayab, babban sakataren kungiyar Kiristocin ta Najeriya ya zanta da Muryar Amurka ta wayar tarho.

“Har ya zuwa yanzu mutanen na tare da ‘yan bindigar, kuma ‘yan bindigar ba su tuntubi kowa ba. A halin yanzu sauran mazauna kauyen sun gudu saboda fargabar ba su san abinda zai faru ba,” inji shi.

Kungiyar CAN ta ce an sanar da ‘yan sandan jihar game da sace mutanen. Amma har yanzu ‘yan sandan ba su fitar da wata sanarwa ba, kuma kakakin ‘yan sandan Mohammed Jalige bai amsa kiran da aka yi masa ba.

Dama dai ‘yan bindiga na cin karensu babu babbaka musamman a karamar hukumar Chikun inda cocin take.

Kakakin kungiyar CAN na kasa, Luminous Jannamike, ya ce “wannan wani mummunan lamari ne mai tayar da hankali. Kungiyar Kiristoci ta Najeriya na sa ido sosai kan lamarin, kuma tana magana da iyalan wadanda abin ya shafa, da kuma hukumomi domin samun karin bayani kan lamarin.

“Yayin da jami’an tsaro suke iya kokarinsu, akwai bukatar a tashi tsaye domin kare wuraren ibada daga miyagu da ‘yan ta’adda,” a cewar Jannamike.

Najeriya na fuskantar kalubalen tsaro da dama, kuma ana yawan samun matsalar satar mutane domin neman kudin fansa.

Masana sun ce tabarbarewar tattalin arziki da matsin rayuwa ke haifar da karuwar rashin tsaro da aikata manyan laifuka.

"Domin kawo karshen hare-hare kan wuraren ibada, yana da muhimmanci gwamnati ta dauki kwararan matakai da suka hada da magance matsalolin zamantakewar al’uma da na tattalin arziki da ke taka rawa wajen rashin tsaro a kasar," in ji Jannamike.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG