A yau asabar dubban mutane ne suka fito titunan birnin Moscow da wasu birane a duk fadin kasar Rasha, domin nuna rashin amincewarsu ga zargin tupka magudi a zaben wakilan Majalisar wakilan kasar, da jam’iyar Prime Minista, United Rasha ta lashe. Matakin da ake ganin baban kalubala ne ga Prime minista Vladimir Putin da jam’iyarsa ta United Rasha wadda take jan ragamar mulkin kasar.
Kasa da sa’a guda bayan an fara zanga zangar, yan sanda suka bada rahhoton cewa akalla mutane dubu ashirin ne suka taru a dandalin Bolchnaya kuda da fadar Kremlin. Su kuma wadanda suka shirya zanga zangar suce mutane dubu arba’in ne suka fito. farko daga gabashin kasar.
Hukumomin birnin Moscow sun baiwa mutane dubu talatin izinin taruwa a wani dandali dake kusa da fadar Kremlin.
Jiragebn sama masu saukar angulu suna shawagi a sararin samaniya a yayinda kuma aka tura motaci jam’in tsaro da yan sanda kwantar da tarzoma a yankin. Zanga zangar ta biyo bayan mumunan murkushe masu zanga zangar da aka yi a farkon wannan makon bayan da jam’iyar Mr Putin ta lashe zaben da aka yi a ranar lahadi.