Dubban Mutane Sun Bace Ta Dalilin Tashin Hankali-Masana

'Yan gudun hijira a yankin Tilabery na Jamhuriyar Nijar

Kungiyar agajin gaugawa ta kasa da kasa ICRC ta yi bayani a game da girman matsalar bacewar al'umma a Nijer tare da jan hankulan jama’a a game da hanyoyin bi don gabatar da koke a ofisoshinta a duk lokacin da wani makusanci ya yi batan dabo.

Dubun dubatar mutane ne suka yi batan dabo a dalilin barkewar tashin hankali a yankunan da suke zaune ko ta wasu dalilai masu nasaba da bala’oin da duniya ke fuskanta ko a bisa dalilan siyasa ko kuma a sakamakon faruwar wani abu na bacin rai wadanda kuma har gaba da yau danginsu ba su da masaniya a game da inda suka shiga ballantana a san halin da suke ciki.

A Jamhuriyar NIjar, kungiyar CICR ko kuma ICRC na kan gaba a yunkurin nemo irin wadanan mutanen don ba su damar sake ganawa da danginsu.

YAN GUDUN HIJIRA

A hirar ta da Muryar Amurka, Madame Laila EDDOUEIB, jami’ar kula da al’amuran da suka shafi mutanen da suka bace da sashen kula da sha’anin bakin haure. ta bayyana cewa, matsala ce mai girman gaske, kuma abu ne da ke tada hankulan iyalan da wani dansu ko mahaifinsu ko miji ko wani danginsu ya bace. Sabili da haka, wajibi ne a taimaki mutanen da suka tsinci kansu cikin irin wannan hali na kuncin rayuwa.

Kasar Nijer ma ba ta tsira daga wannan matsala ba, inda kungiyar agaji ta kasa Red Cross da Red Croissant ta yi rajistar bacewar daruruwan yara sanadiyar matsalolin tsaron da suka addabi yankin sahel inji jami’in hulda da jama’a a kungiyar ta CICR Mahamadou Hama.

Lura da yadda wannan matsala ke kara ta’azzara a wannan kasa ya sa kungiyar CICR ta shiga yunkurin fadakar da jama’a akan hanyoyin da ya kamata iyalan mutanen da suka bata za su bi don gabatar da sanarwa a ofisoshinta.

gudun hijira

Madame Laila tace Red Cross da Red Croissant na da rassa a jihohin Maradi da Tahoua da Agadez da Diffa da Yamai da Tilabery kuma haka a dalilin huldar aikin da ke tsakaninmu da reshen Croix Rouge a Nijer masu aikin sa kai na wannan kungiya da hadin giwar kwamitocin yankuna daban daban na Red Cross na nan domin karbar koke koke a kan wannan batu saboda haka ana iya tuntubar su don sanar da su idan aka sami labaran bacewar wani ko wasu.

A gudummurta ga karrama wannan rana ta tunawa da mutanen da suka yi batan dabo kungiyar ta CICR ta shirya ayyukan dashen itace a manyan biranen jihohin Nijer a matsayin wani matakin kafa alamar ba da dama ga mutanen da makusantansu suka bace su sa ran yiyuwar dangin nasau za su bayyana a watan wata rana.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa, kimanin mutane 580,838 ne suka kwarara zuwa Jamhuriyar Nijar domin neman mafaka sakamkon tashe tashen hankali da ake fama da su a kasashen da ke makwabta da suka hada da Burkinafaso da Najeriya, da kuma Mali.

Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya na nuni da cewa, sama da mutane miliyan uku ne rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a Najeriya.

Saurari cikakken rahoton Souley Barma cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

Dubban Mutane Sun Bace Ta Dalilin Tashin Hankali-Masana