Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sabon Harin ‘Yan Bindiga Ya Raba Dumbin Mutane Da Muhallansu A Jihar Neja


Wuraren da hare-hare ya shafa a harin da 'yan bindiga suka kai a Adamawa
Wuraren da hare-hare ya shafa a harin da 'yan bindiga suka kai a Adamawa

A yanzu haka dai daruruwan mutane ne suka tsere daga garuruwansu a sakamakon wani sabon harin ‘yan bindiga a jihar Neja da ke arewa ta Tsakiyar Najeriya.

Jihar dai tana fama da hare-hare yan bindiga da sace-sace a cikin yan shekarun nan, lamarin da yasa jihar ke da ‘yan gudun hijira a wasu sansanoni.

Rahotanni daga yankin karamar Hukumar Mariga na nuna cewa, yanzu kimanin kwanaki uku ke nan da wadannan ‘yan bindiga suka zagaye garuruwan Kuimo, Masabo, da kuma Sabon Wuri da ma wasu garuruwan da dama da ke wannan yanki.

A hirar shi da Muryar Amurka, wani mazaunin garin Kuimo da ya nemi a sakaya sunan shi ya ce mutanan suna cikin halin firgici, inda a ranar Talata nan sun harbi wani yaro tare da karya masa kafa kuma suna bin gida-gida suna tattara shanu da dama.

Ya kara da cewa, har zuwa yammacin ranar Talata 'yan bindigar na cikin daji kuma jami’an tsaro sun isa wurin amma duka mutane sun watse babu kowa a garuruwan.

Rundunar ‘yan sanda ta jihar Neja ta tabbatar da kai wannan sabon hari, sai dai kwamishinan ‘yan sanda na jihar Neja, Monday Bala Kuryas, ya ce an kara tura karin jami’an tsaro a yankin kuma ya zuwa yanzu al’amurra sun lafa.

Ita ma gwamnatin jihar Neja ta ce tana sane da shigowar wadannan ‘yan ta’adda a wannan yanki kuma tana hada kai da jami’an tsaro domin shawo kan lamarin in ji Sakataren gwamnatin jihar Neja Ahmed Ibrahim Matane.

Wannan sabon hari dai tamkar wata sabuwar barazana ce a wannan yanki, musamman a dai-dai wannan lokaci da damuna ke kunno kai.

Saurari cikakken rahoton Mustapha Nasiru Batsari:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:58 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG