Dubban 'Yan Nijar Sun Taru A Harabar Sansanin Sojan Faransa Da Ke Yamai

Dubban mazauna Birnin Yamai sun fara zaman dirshan na sai yadda hali ya yi a harabar sansanin sojan na Faransa .

Dubban mazauna birnin Yamai sun fara zaman dirshan na sai yadda hali ya yi a harabar sansanin sojan Faransa da zummar tilasta wa gwamnatin shugaba Macron kwashe wadannan sojoji daga kasar ta Nijer. 

A yayin da a yau Asabar 2 ga watan Satumba ya kamata dakarun Faransa 1500 masu yaki da ta’addanci su dakatar da ayyukansu a Jamhuriyar Nijer kamar yadda sojojin juyin mulkin kasar suka ba su wa’adin wata 1, dubban mazaunan birnin Yamai sun fara zaman dirshan na sai yadda hali ya yi a harabar sansanin sojan na Faransa da zummar tilasta wa gwamnatin shugaba Macron kwashe wadannan sojoji daga kasar ta Nijer.

Al'umman Yamai sun fara zaman dirshan na sai yadda hali ya yi a harabar sansanin sojan na Faransa

Yanayin tsamin dangataka a tsakanin kasashen 2 ya samo asali a washegarin juyin mulkin da sojoji suka yi wa zabebben shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan Yulin da ya gabata.

Al'umman Yamai sun fara zaman dirshan na sai yadda hali ya yi a harabar sansanin sojan na Faransa

Wasu masu zanga zangar sun yi bayani ma wakilin Muryar Amurka, Souley Moumouni Barma:

Your browser doesn’t support HTML5

VOX POP FRANCE