NIAMEY, NIGER - Hukumomin Jamhuriyar Nijar sun girke jami’an tsaro a titin ofishin jakadancin Faransa a birnin Yamai inda suke kaddamar da binciken motocin da ke fitowa daga ofishin jakadancin na Faransa bayan da aka umurci ‘yan sanda su tusar keyar Ambasada Sylvain Itte daga kasar.
Tun a yammacin Alhamis aka girke jami’an tsaro a kan titin ofishin jakadancin Faransa da ke unguwar ‘Yantala ta kasa ta nan Yamai sa’oi kadan bayan da aka umurci ‘yan sanda su tusa keyar jakadan zuwa waje.
Jakada Itte ya karya wa’adin da gwamnatin rikon kwaryar Nijer ta ba shi domin ya fice daga kasar.
Jami’an tsaro da suka hada da ‘yan sanda da jandarmomi sun dukufa da binciken motocin da ke fitowa daga ofishin jakadancin na Faransa da wadanda ke fitowa daga gidan jakadan da nufin tantance fasinjoji ko abubuwan da suke dauke da su.
Mai goyon bayan manufofin majalisar soji ta CNSP, Habila Rabiou, ya ce matakin ya yi dai dai.
Yarjejeniyar birnin Vienna ta shekarun farkon 1960 na kwatanta ofishin jakdancin a matsayin wani wurin da ke ba da kariya ga dukkan wanda ke zaune cikinsa.
Moustapha Abdoulaye, wani Kwararre ne a fannin diflomasiya da sha’anin tsaro, ya ce shiga ofishin jakadancin na Faransa domin neman jakadan kuskure ne.
Amma ya ce, tsayawa a waje suna binciken motocin ba laifi ba ne.
A yammacin juma’ar da ta gabata ne ma’aikatar harakokin wajen Nijer ta bai wa jakadan Faransa Sylvain Itte wa’adin awoyi 48 don ficewa daga kasar matakin da Shugaba Macron a take ya yi watsi da shi dalili kenan gwamnatin rikon kwarya ta umurci ‘yan sanda su tusa keyarsa a wani bangare na takun sakar da aka shiga a tsakanin mahukuntan kasashen biyu a sanadiyyar juyin mulkin da kwamandan rundunar dogarawan fadar shugaban kasa Janar Abdourahamane Tchiani ya jagoranci yi wa shugaba Mohamed Bazoum a ranar 26 ga watan yulin 2023.
Wani abin na daban da ke daukan hankali a yanzu haka shine yadda za ta kaya bayan shudewar wa’adin ficewar dakarun Faransa 1500 a gobe asabar 2 ga watan satumba.
Saurari cikakken rahoto daga Souley Moumouni Barma:
Dandalin Mu Tattauna