Dubban Amurkawa Sun Yi Gangami a Birnin Boston

Dubban Amurkawa ne suka yi zanga-zangar nuna adawa da zanga-zangar fadin albarcin baki da masu ra'ayin 'yan mazan jiya suka yi.

Kimanin mutane dubu arba’in ne suka yi dafifi bisa tituna a birnin Boston jihar Massachusetts jiya asabar, a wani gangamin hamayya da na masu gangamin‘yancin fadar albarkacin baki, da ya hada kan masu tsats-tsauran ra’ayin ‘yan mazan jiya da ‘yan zanga zanga da masu jawabai.

Jami’an birnin sun yi fargaban cewa, kishiyoyin gangamin zasu rikide su haifar da tashin hankali, kamar irin wanda aka yi karshen makon da ya gabata a Charlottesville, jihar Virginia, da yayi sanadin mutuwar mutane uku.

‘Yan sanda sun kama mutane uku jiya asabar a wajen zanga zangar bayanda masu gangamin ‘yancin fadar albarkacin baki suka kammala gangaminsu, masu gangamin hamayyar kuma suka fara watsewa suna tururuwa kan tituna kusa da fitaccen wurin shakatawar birnin da ake kira Boston Common.

Dubban mutane da suka yi zanga zangar adawar sun mamaye masu gangamin ‘yancin fadar albarkacin baki da wata kungiya dake kiran kanta “’yancin fadar albarkacin baki ta Boston, ta shirya gudanarwa tun a watan Yuli.

‘yansanda a cikin shirin ko ta kwana sun yi fito mu gama da masu zanga zangar adawar, yayinda suke kokarin ganin dukansu sun nufi wuri guda.

Ba a sami wani tashin hankali ba a gangamin na birnin Boston, ko da yake an nuna hotunan bidiyon a tashoshin labarai inda kungiyoyin masu zanga zangar adawa da dama suka yiwa mutanen da suka sanya hular goyon bayan Donald Trump kawanya, suna yi masu kalaman batanci.