Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Yi Bita Kan Makomar Yakin Afghanistan


Afghanistan Taliban
Afghanistan Taliban

Gwamnatin shugaban Amurka Donald Trump na dab da yanke hukunci kan hanya mafi kyau da zata bi wajen tunkarar yakin kasar Afghanistan da ya kwashe shekaru 16 ana yi.

A yau Juma'a ne shugaba Donald Trump da mataimakinsa da kuma tawagar masu bashi shawara a fannin tsaro zasu gana, domin yanke hukunci kan yakin da ake a Afghanistan.

Kafin wani taro da za a gudanar a yau Juma’a, babban sakataren ma’aikatar tsaron Amurka Jim Mattis, bai bayar da haske ba ga irin yadda wannan tsari zai kasance.

Da yake magana da manema labarai jiya Alhamis a birnin Washington DC, Mattis ya ce “Muna gab da yanke hukunci kuma ina jiran abin da zai fito”

Shugaba Trump zai gana da mataimakinsa Mike Pence da tawagar masu bashi shawara kan harkokin tsaro a Camp David dake jihar Maryland.

Zabin da zasu duba ciki har da aikawa da ‘karin dubban Sojoji zuwa Afhanistan ko kuma Amurka ta janye dukkan sojojinta baki ‘daya, inda zata bar sojojin haya da zasu taimaka wajen gudanar da harkokin tsaro a kasar.

Bayan kwashe shekaru suna samun taimako daga sojojin Amurka da na kungiyar tsaron NATO, sojojin Afghanistan har yanzu sun kasa shawo kan matsalar Taliban, wadanda a baya-bayan nan suka sami shiga yankin iyakar Aghanistan da Pakistan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG