Sakamakon kuri'ar neman jin ra'ayin jama'a a fadin Amurka na baya baya nan, da tashar talabijin ta CNN, da wata kungiya da ake kira ORC suka yi, kuma aka bayyana jiya Laraba, ya nuna Trump, yana kan gaba da maki 21 kan dan takara dake binsa na kusa kusa. Trump ya sami maki 39 cikin dari, wanda ya nuna ya samu ci gaba da maki uku daga kuri'ar neman jin ra'ayi na karshe da aka yi a karshen watan Nuwamba.
Wanda yake bi masa shine Senata mai wakiltar jihar Texas Ted Cruz wanda ya sami kashi 18 cikin dari, wanda ya nuna shima ya sami karin maki biyu.
Sanata Marco Rubio,da kuma likitan kwakwalwa wanda yayi ritaya, Ben Carson, dukkansu sun sami 'yar koma baya-duk suna da maki 10 10, yayinda Gwamnan jihar New Jersey Chris Christie shine yazo na biyar yana da kashi biyar cikin dari. Babu daya daga cikin sauran 'yan takara takwas, karkashin jam'iyyar Republican, wanda aka auna karbuwarsa a wannan safiyon ya sami fiyeda kashi 4 cikin dari.
Jiya Laraba, Trump, ya bayyana farin cikinsa a cikin sakonnin da ya aike ta Twitter, yana cewa "Na gode muku Amurkawa," tare, zamu sake daukaka Amurka".
Tashar CNN da kuma ORC sun gudanar da kuri'ar neman jin ra'ayoyin jama'ar ne tsakanin 17 ga watan Disemba zuwa 21 ga watan.