Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

AMURKA: 'Yan Jam'iyyar Republican Masu Neman Shugabancin Kasar Sun Yi Muhawarar Farko


'Yan Republican goma da suka shiga muhawarar farko
'Yan Republican goma da suka shiga muhawarar farko

Kamar yadda siyasar Amurka take duk mai neman wani mukami wala na zama dan majalisa ko gwamna ko shugaban kasa sai ya tallatar da kansa ta hanyoyi daban daban da doka ta tanada kana ya tsaya zaben fidda gwani na jam'iyyarsa kafin ya tsaya takara.

Jiya Alhamis 'yan takaran neman shugaban kasar Amurka a karkashin jam'iyyar Republican suka yi muhawarar farko tsakaninsu da nufin tallatar da kansu wa amurkawa da zasu yi zaben badi, wato a watan Nuwambar shekarar 2016..

Kamar yadda aka yi zato hamshakin attajirin nan Donalda Trump wanda shi ne kan gaban 'yan takarar 17 ya sha gaban duk sauran. Yayi magana ba tsoro ko jin kunyar kowa. Inda yake shiga ba tan nan yake fita ba kamar yadda aka sanshi da yi.

'Yan takara goma ne suka shiga muhawarar, wato Donald Trump da wasu tara dake binsa a cikin masu farin jinin jama'a.

Sun yi muhawarar ce a birnin Cleveland na jihar Ohio, jihar da take da tasiri a zaben shugaban kasar Amurka wata shida kafin gasar fitar da gwani na zahiri da za'a yi a jihar Iowa.

Donald Trump wanda aka sanshi da fadar albarkacin bakinsa yadda ya ga dama bai ba mara da kunya ba. Da aka tambayeshi ko zai bada tabbacin cewa ba zai tsaya zabe ba a matsayin wanda bashi da jam'iyya idan har jam'iyyarsa ta Republican bata tsayar dashi ba a zaben fidda gwani sai ya ki kememe. Yace "ba zan yi hakan ba yanzu"

Haka ma Trump ya ki ya nemi gafara daga mata wadanda ya kira aladu masu kiba. Ya kuma kirasu karnuka, malalata, masu kazanta kuma yamutsatstsu.

Trump yace babbar matsalar kasar ita ce fadin abun da mutane suke son ji a siyasance. Yace "to gaskiya ba ni da lokacin yin hakan saboda ina son na zama karbabbe a fagen siyasa. Kuma ina fada maku gaskiya wannan kasar ma bata da lokacin yin hakan".

A cikin muhawarar ta awa daya akwai gogaggun gwamnoni kamar su Jeb Bush wanda dan tshohon shugaban kasa ne kuma kanin tsohon shugaba. Akwai Chris Christie gwamnan jihar New Jersey da Rick Perry tsohon gwamnan Texas. Akwai kuma 'yan majalisun tarayyar kasar irin su Rand Paul da dai sauaransu.

To saidai a muhawar yawancinsu sun guji sukar lamirin Donald Trump. Kusan dukansu sun mayar da hankali ne akan shugabancin Obama da kungiyar ISIS, matsalar shige da fice musamman bakin haure da kuma Hillary Clinton wadda suke ganin ita ce zata zamo zakarar jam'iyyar Democrat.

Tsohon gwamnan Texas Rick Perry shi ne ya dan taba Trump inda ya kwatanta matakan da ya dauka akan bakin haure lokacin da yake gwamna da babatun bakin da Trump yake yi yanzu.

Ita ma Carly Fiorina ta dan taba Trump kadan yayin da tace yadda Trump din yake sake manufofinsa kodayaushe ya nuna mutum ne da ba za'a dogara a kansa ba.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG