A yayin da ‘yan Najeriya ke ci gaba da tofa albarkacin bakin su a kan ci gaba da aka samu na jirgin kamfanin Airpeace na farko da ya yi jigilar fasinjoji zuwa Landan a farashi mai sauki daga Naira miliyan 1 da dubu 200 -300, masu kamfanonin shirya tafiye-tafiye na ta bayyana yakinin cewa akwai yiyuwar farashin tikitin kamfanin Airpeace ya yi tasiri wajen kawo sauki a saura kamfanonin tafiye-tafiyen kasashen waje da suke takurawa ‘yan kasar nan da muguwar tsada bada jimawa.
A yanzu dai farashin tikitin karamar kujerar tafiya da dawowa wato economy class na kamfanin Lufthansa daga birnin Legas zuwa Landan kuma Landan zuwa Legas na kan kudi dala dubu 1 da 902.20 kwatankwacin Naira miliyan 2 da 282 idan aka canja dalar a kan Naira dubu 1 da 200, sai kamfanin British airways daga Abuja zuwa Landan a kan naira miliyan 2 da dubu 500 zuwa sama, tashi daga Legas zuwa Landan kuma Naira miliyan 2 da dubu 931.
Sai kamfanin Egypt Air daga Kano zuwa Landan a kan Naira miliyan 2 da dubu 396,352, shi kuma kamfanin Airfrance daga Legas zuwa Landan a kan dala dubu 1 da 234.50 kwatankwacin naira miliyan 1 da dubu 481 da 400 wanda ya yi kusan saukin da kamfanin Airpeace ya samar na Naira miliyan 1 zuwa miliyan 1 da dubu 300.
Wannan matakin na kamfanin Airpeace dai ya yiwa ‘yan Najeriya da dama dadi banda wasu matasa da suka yi ta korafe-korafe a kan kafoffin sada zumunta a game da kalar tufaffin da ma’aikatan cikin jirgi suka sanya wanda bai yi wani tasiri ba in ji wani mai amfani da dandalin X mai suna Afolabi da ya ce abun alfahari ne da ya biya kasa da Naira miliyan 1 da dubu 300 zuwa Landan.
Jagorarar kamfanin shirya tafiye-tafiye na 7Twelve, Hadiza Danu ta yi matukar farin ciki da ci gaban da kamfanin Airpeace ya samar tana mai bayyana cewa akwai yiyuwar saura kamfanonin jiragen saman jigilar fasinjoji na waje su yi koyi da aikin kamfanin na Airpeace.
A nasa bangare kwararre a kan hada-hadar sufurin jiragen sama kuma mai sharhi a kan al’amurran yau da kullum, Mallam Baba Yusuf ya ce dole ne gwamnatin Najeriya ta dauki matakan kare kamfanin Airpeace kuma shi ma kamfanin ya bi dokokin da aka shata a kasar Ingila don gudun abin da ka je ya dawo.
Masu bibiyan al’amurra a dandalolin sada zumunta sun yi ta bayyana cewa an fara samun ragi a farashin tikitin jiragen wasu kamfanonin waje sakamakon sauki a farashin tikitin jigilar farko na kamfanin AirPeace daga Legas zuwa filin saukan jiragen sama na Gatwick wanda alkaluma suka yi nuni da cewa farashin ya fadi daga dala dubu 1 da 580 zuwa $761, amma alkaluma na zahiri da muka tattara daga ofisoshin wasu kamfanonin jiragen sama sun nuna dan akasi cewa ba’a fara ganin ragi kwakwarra ba a kamfanonin British Airways, Lufthansa, Egyptair da dai sauran su ba.
A yanzu dai, kamfanin Air Peace ya fara siyar da tikitin tafiyarsa na zirga-zirgar jiragensa na Landan daga ranar 30 ga watan Maris na shekarar nan lamarin da wasu masu bibiyan lamurra ke nuna fargaba a kan yiyuwar wasu kamfanonin kasashen waje su dakile ayyukan Airpeace din idan gwamnatin Najeriya bata dauki kwararran matakan kare kamfanin nata na cikin gida ba.
Kamfanin Airpeace dai ya yiwa daliban Najeriya dake tafiya Burtaniyya ta jiragensa ragi na musamman da ya kai kaso 15 cikin 100.
Saurari rahoton:
Your browser doesn’t support HTML5