Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Saudiyya, Hadaddiyar Daular Larabawa Sun Goyi Bayan Rage Adadin Man Da Ake Hakowa


Wani taro da OPEC ta yi a birnin Vienna
Wani taro da OPEC ta yi a birnin Vienna

‘Yan siyasar Amurka sun fusata da wannan matsaya da kungiyar ta OPEC ta cin ma, wadda ake ganin za ta kai ga tashin farashin mai.

Saudiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa, sun kare matakin da kungiyar kasashe masu arzkin mai ta OPEC ta dauka, na rage adadin man da ake hakowa.

Kasashen biyu sun bayyana hakan ne duk da cewa, jakadan Amurka ya yi gargadi kan rashin tabbas da tattalin arzikin duniya ke fuskanta.

“Ba wanda yake bin mu bashi…. mun dauki matakin ne da kanmu, domin kyautata makomarmu, saboda haka akwai bukatar mu mutanta wannan matsaya.” Ministan makamashin Saudiyya, Yarima Abdulaziz Salman ya fada a wani taron kasa da kasa da ka shirya a Dubai kan sha’anin man fetur.

A farkon watan Oktoba kungiyar wasu kasashe da Rasha ke jagoranta karkashin kungiyar ta OPEC, ta amince su rage adadin man da ake hakowa da ganga miliyan biyu. Matakin rage adadin man zai fara aiki ne daga sabon watan nan na Nuwamba.

Masu fashin baki a Amurka da nahiyar turai sun yi gargadi kan fuskantar matsalar komadar tattalin arziki a kasashen yammacin duniya da za ta kai ga tashin kudin ruwa da farashin abinci da man fetur, wandanda yakin da Rasha ke yi a Ukraine ta haddasa.

‘Yan siyasar Amurka sun fusata da wannan matsaya da kungiyar ta OPEC ta cin ma, wadda ake ganin za ta kai ga tashin farashin mai.

XS
SM
MD
LG