An kafa dokar hana fita awa 24 wato ba fitar dare da rana a birnin Kano na arewacin kasar Najeriya bayan da wata kungiyar masu tsattsauran ra’ayin Islama ta dauki alhakin kai wasu jerin hare-hare a lokaci guda kan ‘yan sanda da ofisoshin gwamnati.
Bayan da boma-bomai su ka fara tashi kuma aka fara barin wuta da bidigogi, tsoro ya kama mutane, wasu da yawa sun fara gudu a kafa wasu kuma a motoci. Matsalar ta fara ne bayan da wani dan kunar bakin wake ya farfasa tulin boma-bomai a ofishin babban Sufeton ‘yan sanda da ke cikin garin Kano. Jim kadan kuma, sai aka fara jin karar fashe-fashen wasu boma-bomai daga kusan kowane bangare a garin na Kano wanda shi ne na biyu a yawan jama’a a duk fadin kasar. An yi amanna cewa dimbin mutane sun mutu a ciki har da dan kunar bakin waken da kuma sauran maharani da suka mutu bayan musanyar wuta da bindigogin da ta barke tsakanin su da ‘yan sanda.
Wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka Salisu Rabiu, ya ce cikin awa daya da rabi ya kirga karar fashe-fashe sau fiye da 24. Wani babban jami’in hukumar ceton gaggawa ta jahar Kano, Abubakar Jibril shi ma ya bayyana irin rudamin da garin Kano ya shiga ciki bayan hare-haren. Jibril ya shaidawa Muryar Amurka cewa ma’aikatan hukumar su sunkasa kaiwa inda fashewar farkon ta wakana saboda jami’an tsaro sun hana shiga.
Kungiyar ‘yan gwagwarmayar Islama masu tsattsauran ra’ayi ta Jama’atu Ahlus-Sunna LIdda’awati wal Jihad, wadda ake kira Boko Haram ta dauki alhakin kai harin. Wani kakakin kungiyar ya kira ‘yan jarida ya shaida mu su cewa sun kai hare-haren boma-boman a zama ramuwar gayyar kama ‘yan uwansu masu dimbin yawa da aka yi a jahar Kano.