Jerin hare-haren bama-bamai da aka kai birnin Kano dake arewacin Najeriya ya halaka mutane masu yawa.
Rahotanni a kafofin yada labarai sunce an kashe akalla mutane 120 a hare haren da aka kai kan ofisoshin ‘Yan-sanda da na wasu sassan gwamnati.
Kungiyar masu zazzafar ra’ayin addini nin nan ta Boko-Haram ta dauki alhakin kai harin.
An kafa dokar hana fita na sa’o’I 24 cikin birnin na Kano, birni na biyu a girma a Najeriya.
Kamfanin dillancin labaran faransa ya bada labarin cewa an sami wata fashewa a birnin Yenagoa fadar jihar Bayelsa, bayan fashewar ta kano, sai dai babu rahoton fashewar ta jikkata mutane.
A Kanon wani dan kunar bakin wake ya tada nakiyoyi a ofishin kwamishinan ‘Yan sanda. Mintoci bayan haka, sai aka ji tashin wasu fashe fashe a wasu wurare cikin birnin. Dan kunar bakin waken ya mutu a harin, yayin da sauran maharan suma suka rasa rayukansu a mausayar wuta da ‘Yansanda.
Wakilin sashen Hausa a Kano Muhammadu Salisu Rabi’u, yace ya kidaya fashe fashe daban daban 24 cikin sa’a daya da rabi.
Wani jami’in hukumar ayyukan agaji na gaggawa Abubakar Jibril yace ana cikin rudani a birnin. Jibril ya gayawa MA cewa jami’ansa sun kasa isa inda aka kai harin na farko domin jami’an tsaro sun hana su.
Wani kakakin Boko Haram ya gayawa manema labarai cewa harin ramuwar gayyace kan kama ‘yan kyungiyar da hukumomi suka yi a Kano.
Saurari: