Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Najeriya ta yi tayin bada tukuicin Naira miliyan hamsin domin kama Kabiru Sokoto


Kabiru Sokoto, mutumin da ake kyautata zaton yana da hannu a kaiwa wata majami'a harin bom ranar kirsimati a Najeriya
Kabiru Sokoto, mutumin da ake kyautata zaton yana da hannu a kaiwa wata majami'a harin bom ranar kirsimati a Najeriya

A Nigeria, har yanzu ana ci gaba da farautan mutumen nan da akace shine jagoran harin da aka kaiwa kiristoci ranar Kirsemeti, wanda kuma ya arce yayinda yake hannun ‘yansanda

A Nigeria, har yanzu ana ci gaba da farautan mutumen nan da akace shine jagoran harin da aka kaiwa kiristoci ranar Kirsemeti, wanda kuma ya arce yayinda yake hannun ‘yansanda, wanda har gwamnati tace zata bada goron Naira milyan hamsin ko dala dubu 300 ga duk wanda ya taiamaka mata kama shi.

Jami’ai sunce a ranar Laraba ne wannan mutumen da ake kira Kabiru Sokoto ya gudu lokacinda wasu ‘yan bindiga suka shiga artabu da ‘yansandan da yake a hannunsu, zasu kai shi ma’ajiya.

Shugaban Nigeria Goodluck Jonathan dai ya lasa takobin zai kori shugaban ‘yansandan Nigeria Hafiz Ringim daga aikinsa idan har ya kasa faraito Kabiru Sokoto kafin yau Jumu’a. Shi kansa kwamishinan ‘yansandan da ke jagorancin ‘yansandan da suka kamo shi Kabiru din, Zakari Biu, yanzu haka an dakatar da shi daga nasa aikin.

Wannan al’amarin ya kara janyowa ‘yansandan Nigeia zargin cewa su dai kam ba zasu iyatsaron lafiyar al’umma ba, to amma kakakin ‘yansanda Olusola Amore yace suna iya bakin kokarinsu don su sake cafko Kabiru Sokoto.

Aika Sharhinka

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG