Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan bindiga sun kashe turawa biyar a arewacin Habasha


Wasu daga cikin 'yan yawon bude idon da su ka tsira.
Wasu daga cikin 'yan yawon bude idon da su ka tsira.

An hallaka ‘yan kasashen waje masu yawon bude ido su biyar, aka kama biyu,

An hallaka ‘yan kasashen waje masu yawon bude ido su biyar, aka kama biyu, a wani harin da aka kai arewacin Habasha.

Hukumomin Habasha sun ce harin ya auku ne ranar Talata a yankin Afar. Su ka ce an hallaka Jamusawa biyu, ‘yan Hungari biyu da kuma dan Australiya daya a wani harin kwantan bauna – a yayinda wani dan kasar Belgian da kuma wani dan wata kasar su ka sami raunuka.

Hukumomin sun kuma ce an yi garkuwa da wasu Jamusawa biyu da ‘yan Habasha biyu. Kasar Habasha ta ce ‘yan tawaye masu samin goyon bayan kasar Eritrea ne su ka kai harin. Kasar Eritrea dai ta yi watsi da zargin a matsayin karyar banza.

Habasha ta ‘yan kasashen wajen na cikin wani rukunin da ke ziyarar wani yanki mai yawan aman wutar duwatsu a Afar a yayin da aka masu kwantan bauna. An kwashi da yawa daga cikin ‘yan yawon bude idon zuwa Addis Ababa, babban birnin kasar a jiya Laraba, ciki har da wani mutum da ke bisa keken guragu. Da yawansu sun rufe fuskokinsu a yayin da ake kwasarsu cikin motocin hidimomin diflomasiyya.

Kasar Habasha kan zargi makwabciyarta Eritrea da goyon bayan ‘yan bindigan da kan ketara kan iyakarta. Eritrea, wadda ada wani bangare ne na kasar Habasha, ta sami ‘yancin cin gashin kanta a 1991 bayan yaki na tsawon shekaru 30. Wadannan kasashe biyun na ‘yankin tozon Afirka sun gwabza yaki daga baya na rikicin kan iyaka daga 1998 zuwa 2000, kuma har yanzu ana zaman dardar tsakaninsu.

Yankin na Afar dai na da wani dadadden mahakar gishiri, rafuna masu dumi da kuma wuraren da akan yi aman wutar duwatsun da kan ja hankalin masu yawon bude ido. A cikin 2007 an kama wani gungun ‘yan yawon bude ido to amman sai aka sake su daga bisani.

XS
SM
MD
LG