Hukumomin Najeriya sun ce mutumin da ake zargi da hannu a hari da aka kai kan wata majami’a ta darikar katholika a Abuja, ya tsere daga hanun ‘Yansanda, bayan sun kama shi a masaukin jihar Borno dake Abuja.
Sanarwan da rundunar ta bayar jiya talata, tace, ana yiwa mutumin da ake zargin, Kabiru Sokoto, zuwa wani caji ofis na ‘yan sanda dake bayan garin Abuja lokacinda wadansu ‘yan banga suka yiwa ‘yan sandan dake mashi rakiya kwanton bauna, suka kubutar dashi.
Ahalin yanzu dai, an dakatar da kwamishinan ‘yansandan da ya bada umarnin a kai mutumin wani ofishin ‘yansanda. Kuma rundunar tace tana ci gaba da gudanar da bincike kan wannan lamarin.
A wani labari da wata jaridar da ake bugawa a Najeriya da ake kira “The Nation”,da aka buga jiya talata, an ambaci kwamishinan yada labarai na jihar Borno Inuwa Bwala, yana cewa wannan lamari ya kara tabbatar da cewa kungiyar Boko-Harm tana da magoya baya a cikin cibiyoyin tsaro na Najeriya.
Shugaba Goodluck Jonathan ya bayyana irin wannan damuwar a farkon watan nan.