A firarsa da Muryar Amurka Alhaji Maimala Buni yace komi mutum ya yi a shirin dimukradiya dole a samu korafe korafe.
A harakar dimukradiya ba za'a rasa samun koke-koke ba saboda yayinda wani bangare ya samu abu wani bangaren kuma rasawa zai yi.
Dangane da zben ministoci yace babu dalili a ce an sa wani kana wasu su ce lallai lallai a cire a sa wani. Idan an yi hakan mutanen wanda aka cire su ma zasu tashi su yi korafi.
Yace kafin shugaban kasa ya zabo mutanen da ya mika sunayensu sai da ya duba ya dubi cancantansu da tabbatar da sahihancinsu da gudummawarsu da gwagwarmaya da suka yi kuma mutane ne nagari. Mutanen suna da kishin kasa da sadakar da kai kamar shi shugaban kasa.
Abun da talakan Najeriya yake so yanzu shi ne tsamo kasar daga tabarbarewa da ta yi.
Ga karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5