Hukumar bada lamuni ko IMF tana matsawa Najeriya ta kara rage darajar nera saboda yanayin rashin tabbas din makomar kasar a fannin siyasa da tattalin arziki. A nahiyar Afirka Najeriya ce ta fi kowace kasa girman tattalin arziki. Masu sharhi akan alamuran yau da kullum sun nuna rashin jin dadinsu akan jerin sunayen ministocin Shugaba Muhammad Buhari da aka dade ana jira bai kunshi sunan wani fitacce akan tattalin arziki ba. A shekara da ta gabata nera ta fadi da kashi 25 cikin dari haka ma kasuwar hada hadar hannun jari ta komade saboda rashin tabbas din manufar gwamnati da kuma faduwar farashen man fetur a kasuwar duniya da ya shafi kudaden shiga.
Hukumar Bada Lamuni ko IMF Tana Matsawa Najeriya ta Rage Darajar Nera
Wani mai sana'ar canji yana kirga nera a wurin da ake canza kudi inda ake sayan dala daya akan nera 222 maimakon nera 198 a hukumance cikin Legas, ranar 20 ga watan Oktoban 2015.