Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Wasu Kabilun Jihar Yobe Na Korafi Akan Zaben Minista


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Wata sabuwar takaddama ta kunno kai tsakanin kabilun jihar Yobe akan mika sunan Khadiza Abba Bukar Ibrahim da shugaba Munammad Buhari ya yiwa majalisar dattawan Najeriya a matsayin daya daga cikin ministocinsa

Ita Kahadiza Abba Bukar Ibrahim 'yar majalisar wakilai ce dake wakiltar mazabar Damaturu da Gujiba da Gulani da kuma Karmuwa a majalisar wakilan tarayyar Najeriya.

Bugu da kari Khadiza matar tsohon gwamnan jihar ne Abba Bukar Ibrahim wanda shi ma yanzu sanata ne a majalisar dattawa.

Saboda haka ya sa wasu bangarorin jihar suke neman a yi masu adalci domin ita ministar da aka zaba da gwamnan jihar da sakataren APC na kasa duk daga yanki daya suka fito kuma 'yan kabila daya wato Kanuri.Sun nemi shugaba Muhammad Buhari ya sake lale.

Alhaji Sale Zoro Santuraki Fika yana cikin mutanen da suke korafi. Yace suna da yankuna uku ne a jihar. Gwamna da sakataren APC na kasa da ministar da aka zaba yanzu daga yanki daya suke kuma dukansu Kanuri ne.

To saidai Alhaji Zanna Babagana tsohon mai baiwa gwamnan jihar shawara ta harkokin yada labarai yace wadanda suke kin amincewa da zabi tamkar raini ne suke nuna masu. Yace Adamu Ciroma ya yi minista da Adamu Waziri haka ma Bulama amma babu wanda ya yi korafi.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:12 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG