Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dattawa Da Matasa a Gombe Sun Bayyana Goyon Baya Ga Amina


Basu taba samun mace mai halin maza ba irin Hajiya Amina

A yayin da tantance jerin sunayen mutanen da shugaba Muhammadu Buhari, ya gabatarwa majalisar dattawa a matsayin Ministici ke ci gaba da gudana a jahar Gombe kuwa dattawan jihar ne da matasa suka bayana goyon bayan su.

Wasu da daga cikin matasan sun ce “mu mun tabbatar da goyon bayan mu ga Amina, kamar yadda muka tabbatar ita ‘yar jahar Gombe ne muna so mu gayawa duniya cewa muna goyon bayan ta mun zo mu gayawa iyayen kasa cewa mu muna goyon bayan ta”

Su kuwa dattawan sun gudanar da taro ne a dakin gudanar da taro na Amina Ibrahim, in da Yarima Sarkin Bai ya mika godiya ga shugaban kasa a madadin sauran dattawan na zaban kwararu su zama Ministoci a gGwamnatisa.

Shi kuwa Sarkin Gabas din Gombe, Alhaji Hamisu Yagidi Muhammad, ya bayyana cewa basu taba samun mace mai halin maza ba irin Hajiya Amina, wanda ta bautawa Gombe tsakaninta da Allah, da Najeriya wanda shine sanadin da Allah yasa ta daukaka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG