Taron ya hada da gwamna mai ci yanzu Tambuwal da tsohon gwamnan jihar Aliyu Magatakardar Wamako.
A wurin taron jam'iyyar APC ta yi matsaya a hukumance akan zaben minista daga jihar. Sun ki amincewa da zabin Shugaban kasa Muhammad Buhari wanda ya mika sunan Aisha Abubakar zuwa majalisar dattawa domin a tantance ta ya nada ta minista.
Gwamnan jihar Sokoto da sauran manyan jam'iyyar APC da suka halarci taron sun kuduri aniyar fuskantar shugaban kasa tare da majalisar dattawa akan maganar domin su gabatar da matsayin jam'iyyar.
Alhaji Usman Danmadami Isa shi ne shugaban jam'iyyar APC a jihar Sokoto yace ba zasu goyi bayan Aisha Abubakar ba. Yace bata san kowa a jam'iyyar APC a jihar ba. Banda haka karamar hukuma guda ta fito da gwamnan jihar Aminu Waziri Tambuwal. Saboda haka babu hujjar da za'a dauko minista daga yankin.
Amma lamarin na neman haifar da fardiya a jam'iyyar. Wasu bangarorin suna ma kokarin ballewa daga jam'iyyar tare da nuna goyon bayansu da zabin shugaba Buhari.Bangaren shi ne na rusasshiyar jam'iyyar CPC. Sun yi gangami akan rashin amincewarsu da matsayin jam'iyyar APC.
Tsohon shugaban rusasshiyar APC Abubakar Cika Ainun ya jagorancin bangaren dake barazanar ballewa da sunan 'yan kasa masu kishi. Yace tare da Aisha suka yi CPC don haka zargin cewa babu wanda ya santa ba gaskiya ba ne. Yace tana tare dasu tun lokacin da suka fara neman wa shugaba Buhari mulki tun shekarar 2002.
Wasu ma shugabannin jam'iyyar ta APC sun baranta daga matsayin jam'iyyar akan Aisha Abubakar.
Duk da badakalar yau Aisha Abubakar zata bayyana a majalisar dattawa domin tantancewa.
Ga karin bayani