WASHINGTON, D. C. - Cibiyar King da ke Atlanta, wacce Dexter King ya yi aiki a matsayin shugabanta, ta ce ƙaramin ɗan mai fafutukar kare hakkin jama'ar ya rasu ne a gidansa da ke Malibu, jihar California. Matarsa, Leah Weber King, ta fada a cikin wata sanarwa cewa, ya rasu “salun-alun a cikin barci.”
Na uku daga cikin 'ya'ya hudu na Dr. King, Dexter King ya samo sunansa ne daga majami'ar Baptist ta Dexter Avenue a Montgomery, jihar Alabama, inda mahaifinsa ya yi aiki a matsayin limamin makami'ar.
Dexter King yana ‘dan shekara 7 kacal lokacin da aka kashe mahaifinsa a watan Afrilun 1968, yayin da ya ke tallafawa ma'aikatan tsaftar muhalli masu zanga-zanga a Memphis, Tennessee.
Dexter King ya rasu ya bar matar aure da kuma babban yayansa, Martin Luther King III; da kanwarsa, Rev. Bernice A. King; da wata matashiyar ’yar uwa mai suna Yolanda Renee King.
Coretta Scott King ta rasu ne a shekara ta 2006, sai kuma babban dan Dr. King, Yolanda Denise King, a shekarar 2007.
"Kalmomi ba za su iya bayyana bakin cikin da ke zuciyata sakamakon rasa wani ɗan'uwa na ba," in ji Bernice King a cikin wata sanarwa.
Martin Luther King na III ya ce: “Rasuwar tana da babban tashin hankali. Yana da wuya a sami kalmomin bayyana lamari irin wannan a daidai wannan lokaci. Muna rokon addu’ar ku a daidai wannan lokaci ga daukacin iyalan King”.