A ko wace shekara, a ranar Litinin na uku na watan janairu, Amurkawa suna bukin tunawa da Dakta Martin Luther King Jr., jagoran ‘yancin dan Adam da aka kashe wanda ya shirya jerin zanga-zangar lumana tsakanin shekararun 1950 zuwa shekarun 1960 don nuna rashin amincewa da wariyar launi fata, gwagwarmayar nemawa bakaken fata daidaito da ‘yancin kada kuri’a.
Shugaban Amurka Joe Biden zai yi bukin murnar zagayowar ranar tunawa da dan fafukar a Philadelphia, Pennslyvania.
Kamar Yadda ya saba a duk shekara tsawon shekaru uku (3) a jere, bana ma shugaba Biden zai yi aikin sa kai da kungiyar dake bibiyar lamuran masu fama da yunwa na Majalisar dinkin Duniya wato Hunger relief Organisation a Philadelphia, daya daga cikin ayyukan sa kan al'umma da akan yi a ranar hutun a Amurka, Amurkawa suna bukin tunawa da King.
Dandalin Mu Tattauna