Daurin Wata 30 A Kaso Akan Zagin Masauratar Kasar Thailand

Frayim ministan kasar Thailand Yingluck Shinawatra ta na duba paretin sojoji

A cikin watan mayu aka kama Joe Gordon a kasar Thailand

Wata kotun kasar Thailand ta yanke hukuncin daurin watanni 30 ga wani dan kasar Amurka saboda ya rubuta wasu bayanan batunci ga gidan sarautar kasar Thailand.

An tuhumi Joe Gordon da zagin gidan sarautar kasar Thailand lokacin da ya fassara kadan daga cikin tarihin rayuwar sarki Bhumibol Adulyaj da aka haramta a kasar, ya saka a dandalin rubuce-rubucen shi ta intanet.

Gordon Dan kasar Amurka ne da aka haifa a kasar Thailand wanda ke jahar Colorado da zama . A cikin watan mayun da ya gabata aka kama shi lokacin wata ziyarar da ya kai kasar Thailand.

Da farin farko hukuncin daurin shekaru biyar kotun hukunta manyan laifuffuka ta birnin Bangkok ta yankewa Gordon, amma daga bisani ta rangwanta mi shi saboda ya amsa laifi a cikin watan oktoba.

Karamar jakadiyar Amurka a kasar Thailand Elizabeth Pratt ta ce hukuncin yayi tsanani. Pratt ta ce Amurka na girmama masarautar kasar Thailand, amma ta ce haka kuma Amurka ta na goyon bayan 'yancin al'ummar kasar Thailand na furta albarkacin baki.

Lauyan dake kare Gordon ya ce ba zai daukaka kara ba, amma maimakon hakan zai gabatar da bukatar neman ahuwar sarki.