Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugabannin kasashen Turai suna gudanar da wani muhimmin taro a birnin Brussels


Shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel da Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy, da kuma, Shugaban hukumar kasashen Turai Jose Manuel
Shugabar gwamnatin kasar Jamus Angela Merkel da Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy, da kuma, Shugaban hukumar kasashen Turai Jose Manuel

Shugabannin kasashen Turai suna birnin Brussels, suna gudanar da wani muhimmin taron da zai shata makomar takardar kuddinsu ta Euro.

Shugabannin kasashen Turai suna birnin Brussels, suna gudanar da wani muhimmin taron da zai shata makomar takardar kuddinsu ta Euro.

Wasu jami’ai sun bayyana wannan taron da cewa shine dama ta karshe ta warware matsalolin dake addabar takardar kudin ta Euro, wacce dimbin bashin da ake bin kasashen Turan ke janyo mata ci-baya.

Sai dai kuma, tun ma kafin a soma taron aka fara samun sabanin ra’ayi a tsakanin mahalartansa akan yadda za’a tinkari wannan matsalar ta bashi wacce ke barazana ga tattalin arzikin duniya baki dayansa.

Yanzu haka, sha’anin tattalin arzikin kasashen turai sha bakwai dake anfani da wannan takardar kudin ta Euro, ya ja ya tsaya cik, har wasu sun fara hasashen cewa wannan na iya janyo tabarbarewar tattalin arzikin wasu daga cikin kasashen.

Domin magance wannan al’amarin ne yassa shugabar kasar Jamus Angela Merkel da shugaban Faransa Nicolas Sarkozy suka fito suna kira akan ‘yan’uwansu kasashen Turai da su rage yawan kudaden da suke kashewa.

Alkaluma daga watan Janairu sun nuna ana ci gaba da samun hauhawar farashin kayan abinci, na mai da na gidaje da sauransu a Amurka
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 3:02 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

Bayan wasu shekaru kasuwanni na rufe saboda matsalar tsaro a yankin Birnin Gwari na jihar Kaduna, a yanzu harkoki sun fara dawowa
please wait
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p

No media source currently available

0:00 2:31 0:00
  • Auto
  • 240p
  • 360p
  • 480p
  • 720p
  • 810p
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG