Darajar Naira ta kara yin kasa ta yadda a yanzu Dala guda ta kai Naira 206, sannan kuma Fam guda ta kai Naira 300 sannan shi kuma Euro ya kai Naira 330, al’amarin da ke janyo fargaba kan makomar farashin kaya da kuma tattalin arziki.
Da ya ke bayani ga Aliyu Mustafa, wani mai sana’ar canji a Abuja mai suna Mohammed Nura Usman y ace Naira ta fara samun kanta a tsaka mai wuya ne tun wajen watanni uku da su ka gabata. Malam Nura ya alakanta faduwar Nairar da faduwar farashin mai a kasuwannin duniya, kamar yadda ya ce ya ji kwararru na fadi. Ya ce abin na shafar sana’arsu ta canji. Ya ce ‘yan kasuwa ne su ka fi canja dala don tafiye-tafiye kasashen kasuwanci a kasashen waje.
Da Aliyu ya tambaye shi ko ya na ganin alamar faduwar dalar za ta sassauto, sai ya ce babu alamar abin zai yi sauki nan ba dadewa ba, saboda kusan kowace sa’a guda sai ta karu. Ya ce al’amarin ya haddasa tsadar kaya a kasar.
Your browser doesn’t support HTML5