Dangantakar Harkokin Tsaro Tsakanin Kasashe Uku Ta Kara Karfi

Ganawar da aka shirya tsakanin shugaban kasar Amurka Donal Trump, da Firayin Ministan Australia Malcom Turnbull, ta karu da shugaba na uku, Shinzo Abe, na kasar Japan.

Chanjin ya biyo bayan kara karfin dangantakar dake tsakanin kasashen uku ta harkar tsaro musamman yadda zasu maida martini kan shirin Nukiliya, da makamai msu linzami na korea, ta arewa tare da kalubalantar china wacce take kara buga kirji a hanyoyin ruwan dake yankin.

“babban burin mu shine mu tabbatar da dangantaka mai karfi tsakanin kasashen uku domin mu kawo zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin” a cewar shugaban Japan wanda yake hada kai da shugaba Trump, wajen tunkarar Korea ta Arewa.

Ana sa ran fara wani gagarumin atisaye ta ruwa da zai hada da jiragen yakin ruwa na Amurka, uku manya masu daukar jiragen yaki na sama a Wani babban sansanin mayakan ruwa me dauke da jiragen yaki, za’a yi atisayenne a yammacin Tekun Pacific a zaman gwada karfin kasashen.