Shugaban kasar Lebbanon Michel Aoun yayi kira ga kasar Saudiyya data bayyana abinda yasa har yanzu Saad Hariri bai dawo gida ba, bayan ziyarar da ya kai Riyadh, sati guda bayan da yin murabus daga mukamin sa na Prime Ministar wanda yayi ba zato ba tsammani.
Yace wajibi ne kasar ta Saudiyya tayi bayani dalilan da yasa ta hana Prime Minista Hariri komawa Lebanon yaci gaba da kasancewa cikin mutanen sa dama magoya bayan sa.
Yaci gaba da cewa rashin tabbas game da sanin halin da yake cikin ya nuna cewa Kenan kalaman sa, da matsayin da aka danganta shi dashi sun nuna akwai alamar tambaya ciki al’amarin.
Sai dai kawo yanzu Shugaba Aoun bai amince da murabus din Hariri ba a hukumance.
Yace jiya sun tattaubna da shugaban kasar Faransa Emanuel Macron akan wannan batu, wannan ko yana zuwa ne jim kadan bayan da aka ga shi Hariri yana halartan liyafa ta musammam da sarki Salman ya shirya masa a tashan jirgin saman Riyadh.
Facebook Forum