Ma’aikatar harkokin wajen Koriya ta Arewa ta fitar da sanarwarta ta farko a hukumance kan ziyarar da Trump yake a yankin Asiya, tana mai cewa “Wannan ziyara ce ta mai son yada yake-yake musamman ga kasarmu, a kokarin dakile mana garkuwarmu ta Nukiliya.
Koriya ta Arewa dai ta kuma zargi Trump da kokarin mayar da su saniyar ware daga al’ummar duniya, da kuma kokarin gurgunta gwamnatinmu.
Ma’aikatar harkokin wajen ta ce “Irin wannan kalaman gangancin daga tsohon mahaukaci kamar Trump, ba zai taba razana mu ba, ko dakatar da mu ga shirinmu ba.”
Wannan ziyara dai da Trump yake a kasashen Asiya biyar, ta mayar da hankali ne kan Koriya ta Arewa. Trump ya matsawa shugaban kasar China Xi Jinping lamba a wata ganawa da suka yi a asirce kan shirin Nukiliyar Koriya ta Arewa.
Facebook Forum