Gungu-gungun masu ayyukan ceto na ta fama cikin dare, su na ta neman wadanda har yanzu ke da rai, bayan wata girgizar kasa mai karfin 7.3 a ma’aunin girgizar kasa ta girgiza garuruwa da kauyukan da ke kusa da kan iyakar kasashen Iran da Iraki.
Gidan talabijin na Iran ya ba da rahoton cewa mutane wajen 129 sun mutu, a yayin da kuma har yanzu ba a tantance adadin wadanda su ka mutu a cikin kasar Iraki ba.
Girgizar kasar ta auku ne da daren jiya Lahadi a bayan wani birnin Kurdawan Iraki mai suna Halabja, wanda ke daura da kan iyakan kasar Iran. An ji duriyar girgizar kasar har a wurare masu nisa irinsu Turkiyya da Isira’ila.
Bayan girgizar, sai kuma hucin girgiza mai karfin 5.3 ya biyo baya, ta yadda mutanen da ke kauyukan da ke yankin su ka yi ta ficewa daga gidajensu a firgice zuwa kan tituna cikin sanyi da duhu.
Girgizar kasar ta katse wuta da layukan tarho ga garuruwan Iraniyawa da ‘yan Iraki da dama, wanda hakan ya dada jefa ayyukan ceton cikin matsala.
Jami’ai sun yi nuni da yadda akasarin gidajen da ke kauyuka da laka da bulo aka gina su, wanda ya sa su ke da hadarin gaske a duk lokacin da kasa ta girgiza.
Hukumar nazarin girgizar kasa ta Amurka ta ce girgizar kasar ta jiya Lahadi ta auku ne a tsawon lawali mai lahani, wanda ya ratsa kasashen Iran da Iraki.
Facebook Forum