Kwararru kan harkokin Asiya sun ce ba su tsammanin Shugaban Amurka Donald Trump zai dauko batun ‘yancin dan adam da kuma damuwar da ke akwai, game da kashe-kashen mutane ba bisa ka’ida ba a yayin da ya gana yau Litinin da Shugaban Filifinu Rodrigo Duarte.
“Na tabbata ba zai dauko wannan batun ba,” abin da Duarte da kansa ya fada Kenan jiya Lahadi. Kungiyoyin ‘yancin dana dam sun bayyana damuwa game zargin cewa ‘yan sandan Filifinu sun kasa wasu mutane akalla 3,000 da ake zargi da sha da kuma safarar muggan kwayoyi a wani aikin murkushe su da aka yi a fadin kasar – wanda hakan na daya daga cikin alkawurran da Duarte ya yi a yayin yakin neman zabensa.
Duarte ya taba zagin tsohon Shugaba Barack Obama, wanda ya kira shi dan “dan karuwa.” Ya taba bugun kirji ma ya ce shi fa tun ya na dan shekara 16 ya kashe mutum saboda mutumin ya masa kallon raini.
Trump ya isa birnin Manila jiya Lahadi. Masu zanga-zanga kimanin 3,500 sun yi yinkurin tattaki zuwa ofishin jakadancin Amurka amma ‘yan sanda sun hana su. Masu zanga-zangar sun yi ta ihu na bukatar Trump ya bar kasar, su na zargin gwamnatin Amurka, wadda ta yi ma kasar Filifinu din mulkin mallaka na tsawon shekaru 50, da neman haddasa yake-yake a kasashen waje.
Facebook Forum