Dan Najeriya Ya Zama Magajin Garin Colorado Springs

Nigerian businessman and newly elected Colorado Springs Mayor

Yemi Mobolade, dan Najeriya ne kuma dan kasuwa wanda bashi da kwarewa a  harkar siyasa, ya zama bakar fata na farko da aka taba zaba a matsayin Magajin Garin Colorado Springs bayan da yayi nasara akan Wayne Williams da daren Talata a zagayen zaben da aka yi a birnin.

Nasarar Mobolade, ya kasance wani al’amari mai ban mamaki a Colorado Springs mai daddaden tarihin kasancewa cibiyar masu ra’ayin mazan jiya. Wayne Williams wanda ya fafata da Mobolade dan jam’iyyar Republican ne yayin da shi Mobolade kuma yayi takara ba a karkashin wata jam’iyya ba.

Da misalin karfe 7:15 na daren ranar Talata ne Mobolade ya samu kaso 57% na kuri’un da aka kada yayin da Williams ya samu kaso 43% na yawan kuri’un da aka kada bayan kammala kirga kuri’un da aka kada. Williams ya amince da shan kaya da karfe 7:30 na daren Talatan, mintuna 15 bayan ayyana Mobolade a matsayi n wanda ya samu sama da kason kuri'u mafi yawa. ko da ko bayan da aka bayyana sakamakon zaben bayan karfe taran dare, ba a samu wani sauyi a yawan kason 'yan takarar ba.

Mobolade zai gaji John Suthers, wani tsohon mai gabatar da kara a kotu kuma babban attoni janar na Colorado wanda wa’adinsa na zama Magajin Garin birnin na 42 yakai iyaka.

Yanke hukuncin nasarar Mobolade ya na nuni da gagarumin sauyi a siyasar Colorado Springs wanda take da daddaden tarihin kasancewa cibiyar ‘yan siyasa masu ra’ayin mazan jiya. Williams dan jam’iyyar Republican ne yayin da Mobolade kuwa bai tsaya karkashin inuwar wata jam’iyya ba.