Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Za Ta Hana Biza Ga Wasu 'Yan Najeriya


Sakataren Amurka Antony J. Blinken
Sakataren Amurka Antony J. Blinken

Amurka ta sha alwashin hana wasu 'yan Najeriya damar shiga kasarta, sakamakon rawar da suka taka wajen yi wa dimokaradiyya zagon kasa a babban zaben kasar na 2023 da aka gudanar. 

A cikin wata sanarwa da sakataren harkokin wajen Amurka Antony J. Blinken ya fitar, Amurka ta kuduri aniyar tallafawa dimokradiyya a Najeriya da ma duniya baki daya.

“A yau, ina sanar da cewa mun dauki matakin kakaba takunkumin biza ga wasu mutane na musamman a Najeriya saboda zagon kasa ga tsarin dimokradiyya a lokacin zabukan Najeriya na 2023.

Wadannan matakan za su shafi wasu mutane ne na musamman, ba wai takunkumi ne kan al’ummar Najeriya ko kuma gwamnatin Najeriya baki daya ba”.

"Ƙarƙashin sashe na 212(a)(3)C) na Dokar Shige da Fice ta Ƙasa, waɗannan mutane za su fuskanci takunkumi samun biza zuwa Amurka a ƙarƙashin manufar da ta shafi waɗanda aka yi imanin suna da alhakin, ko kuma suna da hannu a wajen tauye dimokraɗiyya. Wadannan mutane na da hannu wajen tursasa masu kada kuri’a ta hanyar barazana da cin zarafi, magudin zabe, da sauran ayyukan da ke lalata tsarin dimokradiyyar Najeriya."

"Daukar matakin sanya takunkumin bizan shiga kasar ya nuna yadda Amurka ta ci gaba da goyon bayan muradun Najeriya na karfafa dimokradiyya da bin doka da oda" a cewar sanarwar.

XS
SM
MD
LG